Heartland za ta karbi bakuncin Enyimba

Ranar Asabar za a buga wasan hamayya tsakanin Heartland da Enyimba a wasan mako na 10 a gasar Firimiyar Nigeria.

Ranar Laraba Enyimba ta doke Bendel Insurance da ci 2-1 a kwantan wasan makon farko.

Kawo yanzu Doma da Lobi Stars da Shooting Stars kowacce tana da 17 a ‘yan ukun farkon teburi.

Enyimba mai maki 18 tana ta takwas din teburi, Heratland kuwa ita ce ta karshen teburi ta 20 da maki shida.

Wasannin mako na 10

Ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba

  • Plateau United da Rivers United
  • Remo Stars da Doma United
  • Heartland da Enymiba

Ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba

  • Lobi Stars da Shooting Stars
  • Kwara United da Gombe United
  • Abia Wwarriors da Rangers International
  • Niger Tornadoes da Akwa United
  • Katsina United da Bayelsa United
  • Kano Pillars da Bendel Insurance

Leave a comment