Xavi ya kasa cin Rayo Vallecano a karo na hudu

Rayo Vallecano da Barcelona sun tashi 1-1 a wasan mako na 14 a gasar La Liga ranar Asabar.

Rayo ce ta fara cin kwallo ta hannun Unai Lopez a minti na 39, haka suka je hutu ana cin Barcelona.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta farke bayan da Rayo ta ci gida ta hannun Florian Lejeune.

Kenan har yanzu Xavi bai yi nasara doke ta ba a La Liga tare da Granada.

Xavi ya yi rashin nasara a wasa biyu da canjaras biyu a fafatawa hudun da ya fuskanci Rayo.

Wasan farko da ya kara da Rayo a Camp Nou, rashin nasara ya yi da ci 1-0, Alvaro Garcia ne ya ci kwallon.

Sun kuma kara haduwa a Camp Nou a wasan farko a kakar 2022/23, inda suka tashi 0-0.

Da Barcelona ta kai ziyara Rayo a kakar da ta wuce a tsakiyar mako suka yi wasan, inda aka doke ta 2-1.

Alvaro Garcia ne ya fara cin kwallo, sannan Fran Garcia ya kara na biyu, yayin da Robert Lewandowski ya zare daya.

Ranar Talata Barcelona za ta karbi bakuncin Porto a wasannin cikin rukuni a Champions League ranar 28 ga watan Nuwamba

Daga nan Atletico Madrid za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na 15 a La Liga ranar3 ga watan Disamba.

Leave a comment