Haaland ya yi atisaye da ‘yan wasan Man City

Erling Haaland ya yi atisaye a shirin da Manchester City ke yi na karbar bakuncin Liverpool ranar Asabar a gasar Premier League.

Tun farko an yi fargabar dan kwallon zai yi jinya mai tsawo, bayan da ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Norway tamaula.

Mai shekara 23 ya ji rauni a wasan da Norway ta doke tsibirin Faroe a wasan sada zumunta.

Yanzu dai Haaland ba zai je Euro 2024, bayan da Norway ta kasa samun gurbin shiga gasar.

Haka shima Rodri, wanda bai buga wasan da Spain ta yi da Georgia ba, yana daga cikin wadanda suka yi atisaye da City.

Kenan ana sa ran Haaland da Rodri za su buga wa City wasan da za ta kara da Liverpool a Etihad ranar Asabar a Premier.

Haaland, wanda ya ci kwallo 13 a bana a wasa 12 a Premier League shi ne kan gaba a cin kwallaye, sai Salah na Liverpool mai 10 a raga.

Leave a comment