Di Maria zai yi ritaya a Argentina bayan Copa America

Angel Di Maria zai yi ritaya daga buga wa Argentina tamaula da zarar an kammala Copa America da za a yi a Amurka.

Dan wasan da ke taka leda a Benfica ne ya sanar da hakan a kafarsa ta sada zumunta.

Mai shekara 35, ya fara yiwa Argentina tamaula a 2008, kawo yanzu ya buga mata wasa 136 da cin kwallo 29.

Ya lashe lambar yabo ta zinare a Olympic a 2008 da Copa America a 2021 da kuma kofin duniya a Qatar a 2022.

Di Maria yana taka leda a Benfica, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar 2024 da cewar za a iya tsawaita masa shekara daya.

Ya dauki Champions League da La Liga da Copa del Rey biyu a Real Madrid.

Ya kuma lashe Ligue 1 guda biyar da Coupe de France a Paris Saint-Germain da kofin lik daya a Portugal tare da Benfica.

Haka kuma Di Maria ya buga wasa a Manchester United da Juventus, shi ne fitatcen dan wasan Argentina a 2014.

Leave a comment