Verstappen bai yadda Hamilton ya koma Red Bull ba

Max Verstappen ya yi watsi da batun da ake cewar Lewis Hamilton zai koma Red Bull suke tsere tare.

Shugaban, Red Bull, Christian Hormer an ji ya fada a kafar yadda labarai ta Burtaniya da cewar tawagar Hamilton sun tuntube su, kan ko suna son aiki tare.

‘Yan wasan biyu sun tattauna da manema labarai a shirin tseren motocin Abu Dhabi Grand Prix da za a yi ranar Lahadi.

Hamilton, wanda bai taka rawar gani ba a kakar nan, ya nesa kansa da batun da Horner ya yi cewar sun tuntube shi.

Dan Burtaniyar ya sanar cewar Horner ne ya yi magana da shi a farkon shekarar nan.

Leave a comment