Sinner ya kai Italy daf da karshe a Davis Cup

Jannik Sinner ya ja ragamar Italy zuwa wasan daf da karshe a Davis Cup, bayan nasara a kan Netherlands 2-1 ranar Alhamis.

Sinner ya yi nasara a karawar dan wasa daidai da na ‘yan wasa bibiyu.

Ya doke Tallon Griekspoor da cin 7-6 (7/3), 6-1, bayan da Botic van de Zandschulp ya yi nasara a kan Matteo Arnaldi 6-7 (6/8), 6-3, 7-6 (9/7) .

A karawar ‘yan wasa bibiyu kuwa Sinner da Lorenzo Sonego suka doke Griekspoor da Wesley Koolhof da cin 6-3, 6-4.

Netherlands, wadda ta kai gurbin ‘yan daf da karshe a 2001, ba ta taba doke Italy ba a shekara 100.

A dai ranar Alhamis din ana sa ran kece raini tsakanin Serbia da Burtaniya a daf da na kusa da na karshe.

Ranar Juma’a ne Australia za ta kara da Finland a daya wasan daf da karshe.

Leave a comment