Awoniyi zai yi jinyar watanni a Nottingham Forest

Kociyan Nottingham Forest, Steve Cooper ya sanar cewar Taiwo Awoniyi zai yi jinyar watanni.

Dan wasan mai shekara 26 ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Najeriya wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

Awoniyi ya ci kwallo 10 Premier League a bana, a wasannin da ya buga wa kungiyar.

Tsohon dan wasan Liverpool, Awoniyi kashin bayan kungiyar ne, wanda ya bayar da gudunmuwa a kakar da ta wuce da ta ci gaba da zama a Premier League zuwa bana.

Najeriya ta tashi 1-1 da Lesotho a Uyo, sannan ta ta kara tashi 1-1 da Zimbabwe a Rwanda.

Rwanda ce ta daya a rukuni na uku da maki hudu, bayan wasa bibiyu, sai Afirka ta Kudu da mai maki uku da Super Eagles mai biyu.

Lesotho da Zimbabwe ma maki bibiyu da su, sai Benin mai maki daya.

Leave a comment