Nmecha zai yi jinya a Dortmund zuwa 2024

Dan wasan Borussia Dortmund, Felix Nmecha zai yi jinya zuwa 2024 kamar yadda koci, Edin Terzic ya sanar.

Terzic ya sanar da manema labarai cewar ‘’Felix Nmacha ba zai buga mana wasa ba har sai 2024, sakamakon raunin da ya ji a kugunsa.

Ya ji rauni a wajen da yake da wuyar sha’ani, saboda haka dole mu bashi dogon lokacin da zai hutu’’.

Nmecha ya koma Dortmund daga Wolfsburg kan ($32.7 million).

Shi ne wanda ya ci Newcastle United kwallo a Champions League a St James Park.

Wanda aka haifa a Hamburg, Nmecha da shi da dan uwansa, Lukas sun girma a Ingila sun kuma yi makarantar koyon tamaula ta Manchester City daga nan suka koma Jamus.

Dortmund tana ta shidan teburin Bundesliga da tazarar maki 10 tsakaninta da Bayern Leverkusen ta daya.

Dortmund za ta karbi bakuncin Borussia Moenchengladbach ranar Asabar a wasan mako na 12 a Bundesliga.

Leave a comment