Real Madrid za ta je gidan Cadiz ranar Lahadi a La Liga

Kungiyar Cadiz za ta karbi bauncin Real Madrid a wasan mako na 14 a gasar La Liga ranar Lahadi.

A yammin ranar a filin wasa na Nuevo Mirandilla za a kece raini tsakanin kungiyoyin biyu.

Hakan ne ya sa Real ke ci gaba da shirin tunkarar wasan, wadda ta yi atisaye biyu, bayan kammala wasannin kasa da kasa.

Carvajal, wanda ya buga wa Spain wasa biyu ya koma atisaye tare da Carlo Ancelotti.

‘Yan wasan sun fara motsa jiki a rufaffen daki daga nan aka fito katafaren filin wasa.

Sun kammala atisayen da salon gudu da kwallo ana bani in baka da gwada gola.

Bellingham ya dan motsa jiki, wanda ya sha fama da jinya, bai yiwa Ingila wasa da Malta da Arewacin Macedonia ba.

‘Yan wasan Real Madrid da ke jinya sun hada da Arda Guler da Tchouameni da Courtois da Militao da Kepa da Camavinga da kuma Vini Jr.

Leave a comment