Tawaga 20 ta samu gubin shiga Euro 2024

Jamus za ta karbi bakuncin kasashe 23 da za su fafata a Euro 2024, kawo yanzu 20 sun samu tikitin buga gasar kai tsaye.

Za a raba jadawalin wasannin ranar 2 ga watan Disamba, inda Jamus mai masukin baki za a hada ta tukunya daya da Portugal da France da Spain da Belgium da kuma England.

A tukunya ta biyu kuwa za ta kunshi Denmark da Turkey da Austria da Hungary da Romania da kuma Albania.

Croatia da Netherlands da Scotland da Slovenia da Slovakia da Jamhuriyar Czech suna tukunya ta uku.

Yayin da tukunya ta hudu ta hada da Italy da Serbia da Switzerland da ukun da za su cike gurbi nan gaba.

Tawaga 12 ce za ta buga wasannin cike gurbi da za a samu uku daga ciki, har da Poland mai Robert Lewandowski.

Wasu daga kasashen har da Kazakhstan da Luxembourg da Israel da Ukraine da Iceland da Wales da sauransu.

Za a raba kasahen zuwa rukuni uku dauke da tawaga hurhudu.

Jamus za ta fara gudanar da Euro 2024 tsakanin 14 ga waan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin badi.

Leave a comment