Birnin Hamburg na shirin kara neman karbar bakuncin Olympic, idan mazauna garin sun amince.
An dakatar da zawarcin da Hamburg ya yi a son karbar wasannin 2024 a 2015, bayan da Munich ya nemi gasar hunturu ta 2022.
Za a gudanar da kada kuria’a 2025, don tantance ko yan garin na son birnin ya karbi bakuncin wasannin Olympic.
Birnin na fatan dawo da gasar Jamus tun bayan wadda aka yi a Munich a 1972.
Yana fatan karbar bakuncin gasar 2036 ko kuma ta 2040.
Wasu biranen da ake cewa za su yi zawarcin Olympic a Jamus har da Berlin da Leipzig da kuma Munich.