Messi da Ronaldo za su fafata a Riyadh Cup

Kungiyar Lionel Messi, Inter Miami da ta Cristiano Ronaldo, Al Nassr za su kara a Riyadh Cup a cikin watan Fabrairun 2024.

Messi mai kyautar Ballon d’Or takwas zai fuskanci Ronaldo, mai biyar jimilla.

Messi mai shekara 36, ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

An gayyaci Inter Miami, domin buga gasar da za a yi da kungiyoyin Saudi Arabia da suka hada da Al-Hilal da Al Nassr, domin lashe Riyadh Cup.

An dai sanar da za a yi wasannin cikin watan Fabrairu, amma ba a tsayar da ranar da za a fara bikin bude gasar ba.

Bayan Messi cikin fitattun ‘yan wasan Inter Miami har da Jordi Alba da Sergio Busquets wadanda suka taka rawar gani a La Liga.

Ronaldo, wanda ya lashe Champions League biyar, yana taka leda a Al Nassr tare da tsohon dan wasan Liverpool Sadio Mane da tsohon kyaftin din Inter Milan, Marcelo Brozovic.

Ita kuwa Al Hilal tana da fitatcen dan kwallon Brazil, Neymar, wanda ke jinya.

A bara a Janairu Ronaldo ya fara taka leda a gasar Saudi Arabia, bayan da ya bar Manchester United.

Leave a comment