Silhavy ya bar kocin Czech duk da samun gurbin Euro 2024

Kocin Jamhuriyar Czech, Jaroslav Silhavy ya sanar da yin ritaya ranar Litinin, bayan da kasar ta samu gurbin shiga Euro 2024.

Jamhuriyar Czech ta doke Moldova 3-0 ranar Litinin ta kuma samu gurbin da za ta buga gasar da Jamus za ta karbi bakunci a badi.

Kociyan mai shekara 62 ya sanar da yin ritaya a wata kafar talabijin ta Czech, lokacin da ake hira da shi bayan tashi daga wasan.

Silhavy ya karbi aikin a 2018, wanda ya kai kasar quarter finals a Euro 2022, amma ya kasa samun shiga kofin duniya a Qatar a 2022.

Kociyan na shan caccaka kan kasa taka rawar gani a rukuni na biyar, wadda ta yi ta biyu, biye da Albania, bayan da ta ci wasa hudu daga takwas da ta fuskanta..

Haka kuma an samu rashin jituwa a cikin tawagar Czech a makon jiya, bayan da aka umarci mai tsaron bayan West Ham, Vladimir Coufal da wasu ‘yan wasa biyu su koma gida, bayan da suka kwana a gidan rawa ranar Asabar.

Leave a comment