Thompson Herah za ta yi aiki da koci Walcott

Daga karshe mai rike da lambar yabo biyar ta zinare a Olympic, Elaine Thompson Herah za ta yi aiki tare da sabon koci Reynaldo Walcott kamar yadda wakilinta ya sanar.

‘Yar wasan na fatan lashe tseren mita 100 da na 200 karo na uku a gasar da birnin Paris zai karbi bakunci a 2024.

Mai shekara 31 za ta je wajen atisayen da za ta yi karkashin Walcott, kamar yadda yake yiwa Shelly-Ann Fraser-Pryce, gwarzuwar duniya karo 10, wadda ta lashe lambar zinare a Olympics a mita 100 a 2008 da a 2008 da kuma a 2012

A farkon watan nan Thompson-Herah ta raba gari da kociyanta, wanda tace ya nemi karin albashi da ya wuce kima.

Thompson-Herah ta lashe lambar zinare a tseren mita 100 da na 2000 a Olympics a Rio a 2016.

Sannan ta kara lashewa a Tokyo har da lambar zinare a tseren mita 100 na ‘yan wasa hudu.

Leave a comment