Southgate ya bukaci ‘yan wasa su kai Ingila ta daya a taka leda

Kociyan tawagar Ingila Gareth Southgate ya kalubalanci ‘yan wasa da su kai kasar matakin farko a kan gaba a taka leda a duniya.

Tuni dai Ingila ta samu gurbin shiga buga Euro 2024, wadda za a saka sunanta cikin ‘yan sawun farko a kwazo a Turai a gasar.

Tawagar Argentina, wadda ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022, ita ce ta daya, sai Faransa ta biyu da kuma Brazil ta uku.

Ingila ta yi kaka biyar tana cikin ‘yan biyar din farko a jadawalin Fifa na wadanda suke kan gaba a murza leda a duniya.

Ana sa ran Ingila za ta yi kasa da Brazil ta koma ta uku, idan Fifa ta fitar da jadawali ranar 30 ga watan Nuwamba.

Southagate na fatan lashe Euro 2024 a Jamus, bayan da Italiya ta yi nasara a kansu a bugun fenariti a 2020 ta dauke kofin a Wembley.

Leave a comment