Marie-Louise Eta ta zama macen farko a aikin koci a Bundesliga

An samu Marie-Louise Eta a matakin farko a horar da tamaula a Bundesliga ranar Litinin a Union Berlin

Ta bayar da horo ga ‘yan wasan a matakin mataimakiyar kociyan rikon kwarya, Marco Grote.

Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta yi atisaye tun bayan da ta sallami kociyanta Urs Fischer, wanda ya ja ragamar kungiyar kaka biyar.

Union ta raba gari da kociyan bayan wasa 14 ba tare da nasara ba, har da doke su karo 13 a dukkan fafatawa, bayan da kungiyar ta yi ta hudu a Bundedsliga a bara, yanzu tana ta karshen teburi.

Mahukuntan Union sun ce ba wani sauri suke sai sun nada sabon kociya ba, kenan Grote da Eta sune za su ja ragamar karawar Bundesliga a karshen mako a wasa da Augsburg.

Fitatcen mai tsaron baya, Leonardo Bonucci bai yiwa Union atisaye ba, sakamakon jinya ranar Litinin tare da David Datro Fofana.

Leave a comment