Cin da Turkiya ta yi mana abin takaici ne – Neuendord

Shugaban hukumar kwallon kafar Jamus, ya ce karbar bakuncin gasar kofin nahiyar Turai, burin ‘yan kasa ne.

Ya kara da cewar doke su 3-2 da Turkiya ta yi ranar Asabar a Berlin, sun ci karo da koma baya.

A hirar da ya yi da Bild TV ya ce ‘’Mune za mu karbi bakuncin Euro 2024, kuma burin da muka dauka shi ne kai wa wasan karshe’’.

Ya ce wasanin da tawagar take yi karkashin Julian Ngelsmann na karfafa gwiwa, wadda za ta buga wasan sada zumunta da Austria ranar Talata na karshe a 2023.

Nagelsmann, wanda ya maye gurbin Hansi Flick ya fara da cin Amurka 3-1 da yin 2-2 da Mexico da kuma doke Faransa yin 2-1.

Doke Jamus da Turkiya ta yi ya nuna karara masu tsaron bayan kasar na bukatar kara karfi tun kan wasannin da za ta karbi bakunci a Yuni zuwa Yulin 2024.

Italiya ce mai rike da kofin, wadda ta lashe Euro 2022, bayan cin Ingila a Wembley a bugun fenariti.

Leave a comment