Novak Djokovic da Jannik Sinner za su fafata a wasan karshe a gasar kwallon tennis ta ATP Finals ranar Lahadi a Turin.
Sinner ya kawo wannan matakin bayan da ya cascara Daniil Medvedev da cin 6-3, 6-7 (4-7), 6-1.
Shi kuwa Djokovic nasara ya yi a kan Carlos Alcaraz da cin 6-3, 6-2 a daya karawar daf da karshe ranar Asabar.
Sinner ya doke Djokovic a karon farko a wasan cikin rukuni ranar Talata a gasar da aka fara tun daga 1970.
Djokovic na fatan lashe kofi na bakwai jimilla a fafatawar da ake yi tsakanin ‘yan takwas din farko, zai haura Roger Federer da daya kenan.