Dan Aliyu zai dambata da na Alin Kawoji a maraba

An tsara wasan gasa a damben Marabar ‘Nyanya da za buga ranar Lahadi a ‘yan tifa da ke Jihar Nasarawa a Najeriya.

An kuma shirya wasannin domin nada Wase Soja a matakin shugaban Kudawan dambe reshen jihar Nasarawa.

Cikin wasannin da za a buga har da na Dan Aliyun Arewa da Bahagon Ali Kawoji, da na Garkuwan Kurma da Rabe Bahagon Ebola.

Haka kuma an tsara wasa tsakanin Autan na Aisha da Bahagon Autan Mamman da wanda za a yi tata burza tsakanin Ramadan da ‘Yar Mage

Haka kuma a kwai wasan da zai yi zafi tsakanin Alin Bata isarka da Shagon Bahagon ‘Yan Sanda da sa zare tsakanin Shagon Lawwali da Boloko da na Garkuwan Duna da Shagon Sanin gidan dan Kande.

Za buga wasannin a ranar Lahadi a damben Safe.

Leave a comment