Sinner ya kai wasan karshe a ATP Finals ranar Asabar

Jannik Sinner ya kai wasan karshe a gasar kwallon tennis ta ATP Finals da ake yi a Turin a Italiya.

Sinner ya yi nasarar doke Daniil Medvedev Daniil da cin 6-7 (4/7), 6-1 a wasan da ‘yan birnin Turin suka marasa baya.

Dan kasar Italiya ya zama na farko da ya kai wasan karshe a ATP Finals ta bana, zai fuskanci ko dai Novak Djokovic ko kuma Carlos Alcaraz ranar Lahadi.

Wannan dama ce ga matashin dan wasan mai shekara 22 ya lashe babbar gasar karshen shekara ta kwallon tennis.

Sinner ya sha tafi daga ‘yan kallo, bayan da ya yi nasara a karawar, bayan da zai jira wasa mai zafi da zai fuskanta.

Djokovic shi ne na farko a jerin wadanda ke kan gaba a buga kwallon tennis a duniya, Alcaraz ne na biyu.

Leave a comment