Southgate na fatan Ingila za ta sa kwazo a Euro 2024

Kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate na fatan za su saka kwazo a gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a badi.

Ingila wadda ta dade ba a doke ta ba ta samu gurbin shiga Euro 2024 da za a yi a Jamus tun saura wasa bibiyu a cikin rukuni.

Ranar Juma’a Ingila ta doke Malta 2-0, hakan ya sa tana cikin manyan tawagogin da darajarsu ke sama a jadawalin da za a yi ranar 2 ga watan Disamba.

Southgate na fatan Ingila za ta kammala wasan karshe na cikin rukuni kuma na karshe a 2023 da cin Macedonia ranar Litinin.

Rabon da a doke Ingila tun cikin Disambar 2022, bayan da Faransa ta yi nasarar cin 2-1 a gasar cin kofin duniya a Qatar.

Faransa tana daga cikin tawaggogin da za su kalubalanci Ingila a gasar da za a yi a Jamus tsakanin Yuni zuwa Yulin 2024.

Hakan ya sa Ingila ta tsara wasan sada zumunta masu zafi da za ta kara a cikin watan Maris da Brazil da Belgium a Wembley.

Leave a comment