Hamilton ya koka da tsare- tsaren Marsandi

Lewis Hamilton bai jure zaman share fage mai wahala a Las Vegas ba, yayin da ya kasa tsallakewa zuwa matakin karshe na fitar da gwani.

Hamilton daya fuskanci fitar sa na uku a shekaran nan da safiyar yau asabar, yayin da yazo matsayi na uku (3) a lokaci mafi sauri.

Hamilton wanda ya lashe zakaran duniya sau bakwai, ya kare a matsayi na uku (3) a duniya, amma dan shekaru 38 ya tabbatar da cewa motarsa tabi ta hanyar da ba ta dace ba.

A koda yaushe akwai bambance-bambance, ”Hamilton ya fada wa kafofin watsa labarai.

Na yi ta fama a lokacin Horo, amma naji daɗi hakan, kuma na fi samun karsashi. Lokaci daya mukayi wasu canje-canje, da banji dadin sa ba a yau.

Leave a comment