Camavinga ya ji rauni a Faransa lokacin atisaye

Dan wasan Real Madrid, Eduardo Camavinga ya ji rauni a gwiwar kafa a lokacin da yake atisaye a tawagar Faransa.

Kamar yadda Faransa ta sanar ranar Juma’a dan wasan ya ji rauni a gwiwar kafarsa ta hagu a lokacin atisaye tare da ‘yan wasa.

Matashin dan kwallon ya koma Sifaniya, domin a auna girman raunin da yaji, tun kan a koma buga gasar La Liga karawar mako na 14.

Kawo yanzu Real ba ta ce ga ranar da zai koma taka leda ba, amma dai raunin gwiwar kafa kan dauki watanni kafin dan wasa ya warke.

Camavinga ya zama kashin bayan Real Madrid a kakar nan, kuma daya daga cikin ‘yan wasan da Real za ta gina kungiyar a kansa tare da Jude Bellingham.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da Girona ke jan ragama da Barcelona take mataki na uku.

Leave a comment