An sokewa EVERTON maki 10

Ranar Juma’a mahukuntan da ke gudanar da Premier League suka sanar da kwashe maki 10 a Everton.

Hakan ya biyo bayan da aka samu kungiyar da laifin karya dokar hada-hadar kasuwanci.

Mahukuntan sun mika lamarin da kwamitin bincike mai zaman kansa a watan Maris kan batun karya dokar cin riba da ta kasha kudi yadda ya kamata.

Everton ta sanar da faduwa a karo na biyar a jere a watan Maris, bayan da ta yi hasarar fam miliyan 44.7 a 2021/22.

An amince kungiyoyin Premier League idan suka yi asarar fam miliyan 105 a cikin kaka uku, amma na Everton ya karya ka’ida.

Everton ta fitar da sanarwar cewar za ta daukaka kara kan wannan hukuncin.

Idan har wannnan hukuncin ya tabbata, Everton ta koma ta 19 a kasan teburin Premier League da maki hudu, iri daya da na Burnley ta biyar.

Leave a comment