Ronaldo ya ci wa Portugal kwallo na 128

Portugal ta je ta doke Liechtenstein 2-0 a wasan neman shiga gasar nahiyar Turai da za a yi a Jamus wato Euro 2024.

Cristiano Ronaldo ne ya fara zura kwallo kuma na 128 kenan da ya ci wa Portugal, sai Cancelo ya kara na biyu.

Tun kan hutu masu masaukin baki sun yi ta kai wa Portugal matsi, wadda tuni ta samu gurbin shiga gasar da za a yi a Jamus.

Ronaldo, wanda ke taka leda a Al Nassr a Saudi Arabia na ci gaba da taka rawar gani a tawagar Portugal, wanda ya ci kwallo 10 a shekarar nan.

Tun can baya Ali Daei na Iraki, shi ne kan gaba a yawan ci wa kasa kwallaye a tarihi a duniya mai 108, yanzu Ronaldo mai 128 ya sha gabansa.

A wasannin da aka buga a rukuni na J, Sloakia ta samu tikitin shiga Euro 2024, bayan doke Iceland 4-2, ita ce ta biyu biye da Portugal a rukunin.

Ita kuwa Luxembourg – wadda za ta buga karawar cike gurbi a badi ta yi nasara a kan Bosnia-Herzegovina 4-1.

Leave a comment