Union berlin ta kori kocinta urs fischer

Union Berlin ta kori kociyanta, Urs Fischer bayan da kungiyar ba ta taka rawar gani a kakar bana.

Kungiyar ta kasa cin wasa 14, sannan ta koma ta karshen teburin Bundesliga.

A wata sanarwa ta kungiyar ta fitar ‘’Union Berlin ta raba gari da Urs Fischer nan take.’’

Kungiyar ta kai ga wanan matakin bayan da shugaban Union Berlin, Dirk Zingler da Fischer suka tattauna ranar Litinin.

A cikin watan Yulin 2018 Fischer ya karbi ragamar horar da kungiyar, wanda ya kai Union Berling gasar Bundesliga a 2019 a karon farko.

A kaka ukun da ya ja ragama a Bundesliga, Fischer ya kai Berlin mataki na bakwai a kakar farko da mataki na biyar a kaka ta biyu da kuma mataki na hudu a kakarsa ta uku.

Ya kai kungiyar Europa League da Champions League a tarihin Union Berlin

Kawo yanzu kungiyar ta sanar da kociyan matasa ‘yan shekara 19, Marco Grote a matakin rikon kwarya.

Leave a comment