An kaddamar da kwallon da za a buga a Euro 2024

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta kaddamar da kwallon da za a buga a gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2024 ranar Laraba.

An gudanar da bikin na musamman a gaban filin wasa da ake kira Olympic a Berlin, wajen da za a buga wasan karske.

Kwallon dai na dauke da launin fari da yawa da digo-digo, dauke da dukkan filaye da za a yi wasannin da sunayen birane 10 da za su karbi bakuncin wasannin.

Kwallon dai na musamman ne, wadda ke dauke da kimiyar da za ta ke fayyace tafiyar kwallon, sannan za a samu sauki wajen yanke hukunci daga masu kula da na’urar taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2024 a Jamus.

Za a yi wasannin a birane 10 da suka hada da Berlin da Cologne da Dortmund da Düsseldorf da Frankfurt da Gelsenkirchen da Hamburg da Leipzig da Munich da kuma Stuttgart.

Leave a comment