Za a gabatar da kwallon da za a buga a euro 2024 ranar Laraba

Golan tawagar Jamus, Manuel Nuer shi ne babban bakon da zai gabatar da samfurin kwallon da za a buga a Euro 2024.

Za a gabatar da kwallon a ranar Laraba, wadda kamfanin Adidas ya kere da za a murza ta a gasar da za a yi tsakanin 14 ga watan Yuli zuwa 14 ga watan Yulin 2024 a Jamus.

Daga nan tawagar Jamus za ta yi atisaye da kwallon a ranar ta Laraba, a shirin da take na buga wasan sada zumunta da Turkiya ranar Asabar, sannan ta kara da Austria kwana uku tsakani.

Mai tsaron ragar Bayern Munich baya cikin ‘yan kwallon da za su buga wa Jamus wasannin biyu, wanda ya sha jinya tun daga Disambar bara.

To sai dai kociyan tawagar Jamus, Julian Nagelsmann ya yi karin haske cewar Nuer zai koma taka leda a wasannin da za suyi a cikin Maris.

Golan Barcelona, Marc Andre ter Stegen ne ya maye gurbin Nuer, wanda ke fatan ci gaba da buga wa Jamus tamaula a matakin farko.

Neur, mai shekara 37, wanda ya koma buga wa Bayern tamaula ya yiwa Jamus dukkan fafatawa a manyan gasar da ta halarta tun daga ta kofin duniya a 2010.

Sauran masu tsaron raga da Jamus ke gayyata sun hada da Kevin Trapp na Eintracht Frankfurt da na Hoffenheim, Oliver Baumann da sabon matashi Janis Blaswich daga RB Leipzig.

Leave a comment