Hojlund da Eriksen BA ZA SU BUGA WA DENMARK WASA BA

Dan wasan Manchester United, Rasmus Hojlund da Christian Eriksen sun hakura da bugawa Denmark wasan neman shiga Euro 2024, sakamkon jinya da suke yi.

‘Yan kwallon biyu sun ji rauni ne a karawar Premier League da United ta ci Luton Town 1-0 ranar Asabar.

Denmark za ta karbi bakuncin Slovenia ranar 17 ga watan nan, sannan ta je gidan Ireland ta Arewacin kwana uku tsakani.

‘Yan wasan United da ke jinya sun hada Lisandro Martinez da Luke Shaw da Tyrell Malacia da Casemiro da Jonny Evans da kuma Amad Diallo.

Leave a comment