Jebitok da Kwemoi sun lashe gudun fanfalaki a Seville

‘Yan kasar Kenya biyu, Edinah Jebitok da Ronald Kwemoi sun lashe gudun fanfalaki da aka gudanar a Seville ranar Lahadi.

‘Yan wasan wadanda a karon farko suka shigar da aka gudanar a Sifaniya, sun yi nasara a kan dan kasar Habasha, Senayet Getachew da dan Kenya, Hillary Chepkwony.

A wasan mata kuwa bayan da wadda ake sa ran za ta lashe gasar ta hakura da karawar sakamakon rauni, ‘yar kasar Habasha ce ta yi nasara wato Getachew da Wede Kefal.

Leave a comment