Djokovic ya kare kakar bana a mataki na daya a tennis

Novak Djokovic zai kammala kakar bana a mataki na daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya, bayan da ya doke Holger Rune a ATP Finals a birnin Turin Italiya.

Mai Grand Slam 24 ya yi nasarar doke Rune da cin 7-6 (7-4) 6-7 (1-7) 6-3 a wasansa na farko a cikin rukuni ranar Lahadi.

Nasarar da Djokovic ya yi ta zama ta 19 a jere a kwallon tennis.

Mai shekara 36 ya lashe Slam uku a 2023, ya zama kan gaba a yawan lashe kofuna a tarihin wasan na tennis a duniya.

Leave a comment