Mbappe ne kan gaba a yawan cin kwallaye a ligue 1

Ranar Lahadi aka kammala wasannin mako na 12 a gasar Ligue 1 ta faransa, inda Paris St Germain ke kan teburi.

PSG, wadda ta yi nasara a wasa takwas daga 12 da ta buga da canjaras uku aka doke ta wasa daya, tana da maki 27.

Ranar Asabar PSG ta je ta doke Stade de Reims da ci 3-0 a karawar mako na 12, inda Kylian Mbappe ya ci kwallo uku rigis a wasan, shi ne kan gaba mai 13 a gasar kwallon Faransa.

Nice ce ta biyu a kan teburin Ligue 1 da maki 26 da tazarar maki daya tsakaninta da PSG da tazarar maki biyu tsakaninta da Monaco ta ukun teburi mai maki 24.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Ligue 1:

Kylian Mbappe   Paris Saint-Germain 13

Akor Adams        HSC Montpellier 7

Mostafa Mohamed     FC Nantes  5

Wissam Ben Yedder    AS Monaco 5

Aleksandr Golovin       AS Monaco 5

Mousa Tamari    HSC Montpellier 5

Leave a comment