Kano Pillars za ta karbi bakuncin Enyimba ranar Lahadi

Kano Pillars za ta kara da Enyimba a wasan mako takwas a Firimiyar Najeriya a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata ranar Lahadi.

Kafin nan ranar Asabar Doma United za ta karbi bakuncin Akwa United a wasan mako na takwas a gasar Firimiyar Najeria.

Doma United mai maki takwas tana ta 12 a kan teburi, ita kuwa Akwa mai maki bakwai tana ta 17 a kasan teburi.

Kano Pillars mai maki tara tana ta 10 teburi, ita kuwa Enyimba tana mataki na 16 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Najeria mai maki bakwai.

Wasan da za a buga Asabar Asabar ga watan Nuwamba

  • Doma United da Akwa United

Wasan da za a kara Lahadi 12 ga watan Nuwamba

  • Kwara United da Shooting Stars Sports Club
  • Sunshine Stars da Rangers International       
  • Katsina United da Rivers United  
  • Lobi Stars da Sporting Lagos         
  • Niger Tornadoes da Bendel Insurance 
  • Kano Pillars da Enyimba      
  • Remo Stars da Gombe United      
  • Plateau United da Abia Warriors

Leave a comment