An sanar da ranar wasan Barcelona da Atletico

Ranar Talata hukumar da ke gudanar da La Liga ta sanar da cewar za a buga wasan mako na 15 a La Liga tsakanin Barcelona da Atletico Madrid ranar 3 ga watan Disamba.

Za a buga karawar ta hamayya ranar Lahadi a filin Estadi Olímpic Lluís Companys.

Barcelona za ta yi wasan kwanaki kadan bayan ta karbi bakuncin Porto a Champions League a Estadi Olímpic, sannan ta yi wasa da Girona a gida a karshen mako.

Kenan kungiyar da Xavi Hernandez ke jan ragama za ta yi wasa uku a gida a jere cikin sama da mako daya.

Barcelona mai maki 27 tana ta ukun teburi, yayin da Atletico mai kwantan wasa daya take ta hudun teburi mai maki 25.

Girona ce ta daya mai maki 31 da Real Madrid ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da ta dayan teburin.

Wasannin mako na 13 da za a buga a La Liga:

Ranar Juma’a 10 ga watan Nuwambar 2023

  • Athletic de Bilbao da Celta de Vigo  

Ranar Asabar 11 ga watan Nuwambar 2023

  • Rayo Vallecano da Girona     

  • UD Almeria  da Real Sociedad 

  • Osasuna da Las Palmas    

  • Granada da Getafe

  • Real Madrid da Valencia

Ranar Lahadi 12 ga watan Nuwambar 2023

  • Real Mallorca da Cadiz

  • FC Barcelona da Deportivo Alaves    

  • Sevilla da Real Betis Match details

  • Atletico de Madrid da Villarreal

Leave a comment