Taylor zai busa wasan Chelsea da Man City a Premier League

Anthony Taylor zai busa wasan Premier League ranar Lahadi a karawar da Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester City, duk da an yi masa hukuncin komawa busa gasar Championship.

An hukunta tashi ne, bayan fenaritin da ya bai wa Newcastle United mai takaddama da ta farke wasan da ta tashi 2-2 a gidan Wolverhampton.

Taylor ya yanke hukuncin cewar Hwang Hee Chan ya taba Fabian Char, amma da aka duba lamarin a faifan bidiyo sai aka ga dan kadan ya taba shi bada nufin keta ba.

Leave a comment