Camavinga zai ci gaba da wasa a Real Madrid zuwa 2029

Dan wasan tawagar Faransa, Camavinga ya saka hannun kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a santiago Bernabeu zuwa 30 ga watan Yunin 2029.

Wanda ya koma kungiyar Sifaniya a 2021 yana dan shekara 18, ya lashe kofi shida a Real Madrid a kaka biyun da yake taka mata leda.

Cikin kofunan da ya dauka sun hada da Champions League da Club World Cup da European Super Cup da La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.

Mai shekara 20 har ya buga karawa 114 a Real Madrid tun bayan da ya koma kungiyar daga Rennes ta Faransa.

Ya shiga takarar matashin dan kwallo ta Golden Boy a 2021 da kuma 2022 don lashe kayutar Kopa Trophy.
 

Leave a comment