Chelsea ta kawo karshen wasa 10 ba a ci Tottenham ba

Tottenham ta yi nasara a gida da ci 4-1 a hannun Chelsea a karashen wasa na 11 a gasar Premier League ranar Litinin.

Tottenham ce ta fara cin kwallo minti shida da fara wasa ta hannun Dejan Kulusevski, kafin hutu Chelsea ta farke ta hannun Cole Palmer a bugun fenariti.

Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu ne sai aka bai wa dan wasan Tottenham, Cristian Romero jan kati, sannan aka kara korar mata

Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu ne sai aka bai wa dan wasan Tottenham, Cristian Romero jan kati, sannan aka kara korar mata Destiny Udogie.

Hakan ya sa Chelsea ta samu damar kara kwallo uku, inda Nicolas Jackson ya ci ukun rigis.

Hakan ne ya kawo karshen wasa 10 da Tottenham ta yi ba tare da an doke ta ba a gasar Premier League ta bana karkashin sabon koci, Ange Posteglou.

Tottenham, wadda ta fara kakar nan da kwarin gwiwa ta ci wasa takwas da canajaras biyu, sai a wasan mako na 11 ne Chelsea ta doke ta.

Tsohon kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino shi ne ya ja ragamar Chelsea ta je ta yi wannan namijin kokarin a ranar Litinin.

Da wannan sakamakon Manchester City ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 27, sai Tottenham mai maki 26 da kuma Liverpool ta uku da maki 24.

Chelsea, wadda ta fara kakar bana da fuskantar kalubale, ta hada maki 15 ta koma ta 10 a teburin Premier League.

Leave a comment