Autan na Aisha ya doke dan aliyu ya ci mota

Ranar Lahadi Autan na Aisha ya buge Dan Aliyu ya lashe mota a marabar N’yanya a jihar Nasarawa, Nageriya.

Tun a makon da ya gabata aka sa mota tsakanin dan damben Guramada da na Arewa a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke ‘yan tifa a karamar hukumar Karo.

Tun farko sai da makadan ‘yan dambe Labaran dan Gwamba ya wake ‘yan wasan biyu, wadanda magoya baya suka yi musu alherin da zai kara musu kwarin gwiwa.

Bayan nan ne suka shiga filin wasa, inda alkalin wasa Anas dan Dume ya daga hannunsu da cewar suna za su buga damben gaba.

Daga nan suka taka dambe tsakanin Autan na Aisha da Dan Aliyu, kuma a turmin farko Autan na Aisha ya yi kisa.

Dan damben Guramadan ya sha ruwan kudi daga magoya baya, wadanda suka ji dadin jarumtar da dan wasansu ya yi.

Auta na Aisa ya yi sama da wata biyar a maraba ba tare da an buge shi ba.

Leave a comment