Ko Diego Simeone zai ci gaba da zama kocin Atletico Madrid?

Ana ta tantancewa kan makomar Diego Simeone a Atletico Madrid, bayan shafe sama da shekaru 14 yana jan ragamar ƙungiyar.

Wasu rahotanni na nuni da cewa Simeone na iya ci gaba da zama na ɗan lokaci kafin a ɗauki sabon koci, sai dai ana ganin hakan ba shi da tabbas idan aka kammala kakar wasa ta bana.

Sai dai a wani bangare, ana ganin ƙungiyar za ta iya ƙara masa kwantiragi na shekara guda, wanda zai kai shi har zuwa ƙarshen kakar 2026/27, duba da irin gudunmawar da ya bayar tsawon lokaci.

A halin yanzu, yarjejeniyar da Simeone ke da ita da Atletico na ba shi damar barin ƙungiyar bayan kammala kakar nan, amma ana sa ran shugabannin kulob ɗin ba za su amince ya ajiye aiki a yanzu ba.

A kakar bana, kocin mai shekara 55 ya jagoranci Atletico zuwa nasarori masu muhimmanci, inda kuma ƙungiyar ke fafatawa a gasar UEFA Champions League, inda za ta kara da FC Barcelona a zagayen kwata fainal.

A gasar La Liga, Atletico na mataki na huɗu da maki 57 daga wasanni 26, bayan samun nasarori 17, canjaras shida da kuma rashin nasara shida.

Ranar Asabar 4 ga watan Afirilu, Atletico za ta karɓi bakuncin Barcelona a La Liga, kafin daga bisani ta je Camp Nou domin buga wasa na gaba a gasar zakarun Turai.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top