An ɗage wasan PSG da Lens domin karawar Liverpool a Champions League

Mahukuntar gasar Ligue 1 sun amince da ɗage wasan da Paris Saint-Germain za ta yi da Lens, domin bai wa PSG damar shirya karawarta da Liverpool a gasar UEFA Champions League.

Tun farko, PSG za ta kara da Toulouse a Ligue 1 ranar 3 ga watan Afirilu, kafin ta karɓi bakuncin Liverpool a wasan zagayen kwata fainal na Champions League ranar 8 ga watan Afirilu.

Bayan wannan wasa, PSG za ta sake fuskantar Lens a Ligue 1 cikin kwanaki uku, kafin ta je filin Anfield domin buga wasa na biyu ranar 14 ga watan Afirilu.

Saboda cunkoson jadawalin wasanni, PSG ta nemi a ɗage wasan da Lens domin ta mayar da hankali wajen fafatawa da Liverpool.

A bara ma, PSG ta yi nasarar fitar da Liverpool daga gasar, kafin daga bisani ta kai ga lashe kofin Champions League a karon farko a tarihinta.

Hukumar Ligue 1 ta tabbatar da cewa an mayar da wasan PSG da Lens zuwa ranar 13 ga watan Mayu.

Haka kuma, an sauya ranar wasan da RC Strasbourg za ta yi da Brest, saboda wasu sauye-sauye da suka shafi jadawalin wasanni.

A halin yanzu, PSG ce ke jagorantar teburin Ligue 1 da maki 60, tana da tazarar maki ɗaya kacal a kan Lens wadda ke matsayi na biyu.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top