Ƙungiyar Sevilla ta kori mai horar da ita, Matias Almeyda bayan jan ragama wasa 32 a dukkan karawa.
Hakan ya biyo bayan da ƙungiyar ta sha kashi a gida a La Liga 2-0 a hannun Valencia.
A ranar Litinin Sevilla ta sayar da korar kocin a shafinta na Intanet da kuma yi masa godiya.
Ɗan kasar Argentina ta ci wasa 10 da canjaras bakwai aka doke shi 15 daga 32 da ya ja ragama.
Haka kuma a karkashin Almeyda, Sevilla ta ci ƙwallo 43 aka zura mata 52 a raga.
Daga ciki an zura wa Sevilla 49 a raga a La Liga, sakamako mafi muni a kakar nan, duk da ta ci 37 a gasar.
Sevilla tana ta 16 a kasan teburin La Liga da maki 31 daga wasa 29 da ta buga kawo yanzu.
Cikin gasar La Liga ta yi nasara takwas da canjaras bakwai aka doke ta wasa 14.
Ranar 5 ga watan Afirilu, Sevilla za ta je gidan Real Oviedo, domin buga mako na 30 a La Liga.