Guardiola ya zama na farko da ya ci Carabao Cup biyar

Manchester City ta doke Arsenal 2-0 ta ɗauki Carabao Cup a Wembley ranar Lahadi.

City ta ci ƙwallon ta hannun Nico O’Reilly a minti na 60, sannan ya kara na biyu mintu huɗu tsakani.

Da wannan sakamakon Pep Guardiola ya zama na farko da ya ɗauki League Cup biyar jimilla.

Sai dai Arsenal ta ci gaba da ƙamfar kofi tun daga FA Cup da ta dauka a 2020, rabon ta da Carabao Cup kaka 33.

Arsenal ta rasa ɗaya daga kofi huɗun da ta sa ran ɗauka a bana, saura FA Cup da Premier League da Champions League ke gabanta.

Kawo yanzu tana ta ɗaya a teburin Premier League da tazarar maki tara tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Sai dai Gunners ta buga wasa 31, yayin da ƙungiyar Etihad ta yi karawa 30 a Premier League.

Ranar 4 ga watan Afirilu, Arsenal za ta je Southampton a FA Cup kwana uku tsakani ta je Sporting.

Arsenal za ta ziyarci Portugal a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top