Barcelona ta doke Rayo Vallecano 1-0 a wasan mako na 29 a La Liga ranar Lahadi.
Ta kuma ci ƙwallon a minti na 24 ta hannun Ronald Araujo a filin wasa na Camp Nou.
Da wannan sakamakon Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki bakwai.
Idan anjima Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid a wasan hamayya a Santiago Bernabeu.
Koda Real Madrid ta yi nasara a kan Atletico zai zama saura maki huɗu tsakaninsa,
Karshen mako babu gasar La Liga, za a buga wasan kasa da kasa, wato International Break.
Kenan sai a makon farko a cikin watan Afirilu, Barcelona za ta je Atletico Madrid a La Liga.
Kwana huɗu tsakani za su sake fuskantar juna a Champions League a kwata fainals.