Barcelona ta kai kwata fainal a Champions League, bayan caskara Newcastle United 7-2 ranar Laraba.
Kenan ƙungiyar Sifaniya ta kai zagayen ƴan takwas a gasar ta zakarun Turai da cin 8-3 gida da waje.
Barcelona ta ci ƙwallayen ta hannun Raphinha da ya ci biyu da Marc Berna da Lamine Yamal da Fermine Lopez da kuma Robert Lewandowski da shima ya zura biyu a raga.
Ita kuwa Newcastle daga England ta ci ƙwallo biyu ta hannun Anthony Elenga.
Ga dalilai biyar da Barcelona ta yi waje da Newcastle United:
1. Ƙarfin hari (Attacking Power)
Barcelona ta nuna ƙarfi sosai a gaba, inda ‘ƴan wasanta suka riƙa kirkirar damarmaki da yawa. Hakan ya sa suka zura ƙwallaye da dama cikin sauƙi.
2. Mallakar ƙwallo (Possession Game)
Salon wasan Barcelona na riƙe ƙwallo ya hana Newcastle samun damar kai hare-hare.
Hakan ne ya sa suka fi rinjayar wasan daga tsakiya, kuma suna sarrafa tamaula yadda suke so.
Barcelona tana da kaso 63 cikin 100 na rike wasan, ita kuwa Newcastle tana da 37.
3. Raunin mai tsaron ragar Newcastle
Mai tsaron ragar Newcastle Aaron Ramsdale, ya yi kura-kurai da yawa a fafatawar a Camp Nou.
Ya yi ta kokarin daƙile hare-haren Barcelona, wanda ya bai wa ƙungiyar Spain damar cin ƙwallaye cikin sauƙi.
An buga masa kwallo 18 daga ciki 13 suka nufi raga aka zura masa bakwai a raga.
4. Kwarewar ƴan wasa
Ƴan wasan Barcelona sun fi nuna ƙwarewa da gogewa, musamman a manyan wasanni irin wannan.
Wannan ya ba su damar sarrafa wasa da kuma amfani da damar da suka samu da cewa a Camp Nou suke.
5. Tsarin koci (Tactics)
Kocin Barcelona, Hansi Flick ya fi na Newcasle, Eddie Howe gogewa a irin wannan matakin, bayan da yake da kofuna Champions League.
Hakan ya sa ya tsara dabarun kai hare-hare da sauri, inda ya yi anfani da raunin Newcastle, musamman ta bangarorin filin
Yanzu dai Barcelona ta kai zagayen kwata fainal, ita kuwa Newcastle sai ta koma gida ta yi fatan karewa cikin ƴan huɗun farko a teburin Premier League.
Haka ne zai sa ko za ta samu damar sake buga Champions League a baɗi.
Newcastle tana mataki na tara a teburin Premier League da maki 42, bayan wasan mako 32.
Ita kuwa Barcelona tana ta ɗaya a La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.