Mbappe da Bellingham za su buga wasan Man City a Etihad

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real Madrid ta samu karin ƙwarin gwiwa, sakamakon da Kylian Mbappe da Jude Bellingham za su iya buga mata wasan da za ta yi da Manchester City ranar Talata a Etihad.

Ƙungiyar ta Sifaniya za ta ziayrci ta Ingila, domin buga wasa na biyu a Champions League karawar zagaye na biyu, yayin da Real Madrid ta ci 3-0 ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Mbappe ƙyaftin ɗin tawagar Faransa ya ci rauni tun farko farkon watan Maris, wanda ya rabon ya taka leda tun wasan Osasuna ranar 21 ga watan Fabrairu a La Liga.

Shi kuwa ɗan wasan tawagar Ingila, ya ci rauni a minti na 10 da fara wasan da Real Madrid ta yi da Rayo Valecano ranar 1 ga watan Fabrairu a gasar ta La Liga.

Tun farko an yi hasashen cewar Bellingham zai yi jinyar mako huɗu, har wasu ke cewa da ƙyar ne idan zai buga wa Ingila wasan sada zumunta da Uruguay da Japan a cikin watan nan.

Real Madrid ta kawo mataki na biyu a Champions League, bayan buga karawar cike gurbi da Benfica, ita kuwa City ta kai zagayen gaba kai tsaye ne daga fafatawar cikin rukuni.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top